A cikin shirin za ku ji cewa suhgabannin kasashen manbobin kungiyar Ecowas ko Cedeao sun radawa kudaden bai daya kasashen ke son soma amfani da su suna, kana kuma a wannan rana ta Lahadi ce ake soma kada kuri'a a zaben kananan hukumomin da ake gudanarwa a kasar Togo, sai dai mata da maza matasa sune suka mamaye zaben.