A cikin shirin bayan labaran duniya za ku ji a wannan Lahadi Jamusawa ke zabar wanda zai samu nasara wajen maye gurbin shugabar gwamnati Angela Merkel. Mutanen Legas na Najeriya na duba alakarsu da gwamnatin Jamus karkashin Angela Merkel. A Nijar an yi wani babban taron haddadiyar kungiyar kwadagon kasar wato USTN a birnin Yamai. Akwai rahoton Himma dai Matasa da Sharhunan Jaridun Jamus.