Sakataren tsaron kasar Amirka Jim Mattis ya baiyanawa shugabannin kasashen Larabawa cewar kisan 'Dan Jarida Jamal Khashoggi a cikin karamin ofishin Jakadancin Saudiyya dake birnin Santanbul al'amari ne da shafi kowanne bangare kuma Amirka ba zata lamunci yadda aka gana masa azaba don a rufe masa baki ba.