1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin sasantawa da 'yan Taliban a Afghanistan

Usman Shehu Usman MA
December 31, 2019

Ga dukkan alamu, kungiyar Taliban a Afghanistan na son cimma yarjejeniya da gwamnati a kan tsagaita buda wuta. Sai dai hakan zai dogara ne da sako wa 'yan bindigar da ke tsare.

https://p.dw.com/p/3VXOt
Pakistan Treffen des Außenministers mit den Taliban
Zaman tattaunawa da kungiyar Taliban da aka yi a bayaHoto: picture-alliance/AP Photo/Pakistan Foreign Office

A zahiri dai yanzu kam kungiyar Taliban so take ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a Afganistan. Hakan kuwa in ya samu zai sa al'ummar kasar da yake ya daidaita su samu sararawa. To sai dai fa ana saran in har yarjejeniyar ta samu, to za a sako dararrun mayakan Taliban da ke a gidajen kaso.

A hukumance dai batun musayar fursunoni baya cikin jadawalin tattaunawar da ake yi a Doha. To sai dai kamfanin dillacin labarai na AP, ya ruwaito cewa Kungiyar Taliban ta mika wa Amirka sunaye 5000 na mayakanta da ke daure, wanda ake son a tattauna makomarsu.

Russland l Politischen Führer der Taliban treffen zu Gesprächen in Moskau ein
Wasu kusoshin kungiyar TalibanHoto: picture alliance/AP Photo/A. Zemlianichenko

Ko da yake ba a san adadin ‘yan taliban da yanzu haka ke daure ba, amma wani gidan yari daya da ke Kabul, an yi kiyasin mayaka 3000 ne ke daure, ciki har da daya daga cikin shugabanninsu wato Maulvi Niaz Muhammad, wanda jaridar AP ta yi hira da shi.

 

"Samun yanci shi ne abu guda da muke fata. A nan ana nuna mana wariya, ana gana mana azaba. A duk lokacin dan karamin abu ya faru sai anan tsaiwaita wa'adin zamanmu, wasu lokutan har karin shekara guda"

Daya dan Taliban da ke daure wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya tabbatar gana musu azaba da ake yi a gidan yarin.

"Abokananmu da yawa an kashe su a nan cikin gidan yari. A bisa abu kalilan masu gadin gidan yarin sai su yi ta lakada mana duka, a raunata mu har ma da kisa. Wannan ya sha faruwa"

Gidan yarin na tsakiyar birnin Kabul shi ne mafi girma a Afgahnistan. Kuma akwai tabbacin ana matukar gana azaba wa fursunoni. Sau da dama an nemi fasa gidan yarin, Allah kadai ya san jinin da aka zubar a ciki  aa wajensa lokacin neman fasa shi. An gina gidan yarin a shekarun 1970, a lokacin bisa adadin mutane dubu biyar aka yi shi, amma yanzu sama da mutun dubu 10.000 ke a ciki. Amma a cewar daraktan kula da gidan yarin Akhtar Mohammad Noorzoy, ana kula da 'yan Taliban kamar sauran fursunoni.