1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin sasantawa tsakanin Koriyoyi biyu

Yusuf Bala Nayaya
January 5, 2018

Koriya ta Arewa da takwararta Koriya ta Kudu sun amince su fara tattaunawa kan hadin kai a shirin wasannin Olympic lokacin hunturu, dai dai lokacin da Amirka ta ce za ta tsayar da atisayen soja da Koriya ta Kudu.

https://p.dw.com/p/2qOoE
Nordkorea Kim Jong-un
Hoto: Getty Images/AFP/KCNA

A wannan Juma'ar, Koriya ta Arewa ta aika sako zuwa ga takwarar tata Koriya ta Kudu inda ta bayyana amincinta da shirin tattaunawar na garin Panmunjom da ke kan iyakar kasashen biyu a ranar Talata don tattaunawa kan shirin na gasar Olympic da ma tattauna alakar kasashen biyu.

Mahukuntan na birnin Seoul na Koriya ta Kudu, sun bayyana cewa takwarorin nasu na Arewa sun amince da shirin tattaunawar ne kan wasannin, sa'o'i bayan da Amirka ta bayyana cewa za ta tsagaita shirin atisaye da sojan kasarta tare da takwarorinsu na Koriya ta Kudun za su yi na shekara, har sai an gama wasannin na Olympic.  A karon farko kuma an yi magana tsakanin Shugaba  Moon Jae-in na Koriya ta Kudu da Donald Trump na Amirka ta wayar tarho, tun bayan jawabin sabuwar shekara da Shugaba Kim Jong-un na Koriya ta Arewa ya yi inda ya ce kunamar makamin nukiliyarsa na kan teburinsa. Sai dai kuma ya ce a shirye 'yan wasan kasarsa suke su je wasannin na Olympic don haka Koriya ta Kudu ta mika masu goron gayyata kuma sun aminta da lamarin da ya karfafa gwiwar mahukuntan a cewar Yoon  Young-Chan babban sakataren hulda da jama'a na shugaban kasar Koriya ta Kudu.

Shugaba Moon Jae-in na Koriya ta Kudu yana jawabi
Shugaba Moon Jae-in na Koriya ta Kudu yana jawabiHoto: picture-alliance/Yonhap

Ita ma dai kasar China da ke zama babbar kawa ga Koriya ta Arewa a wannan Juma'a mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajenta Geng Shuang ya bayyana cewa wannan mataki da aka cimma abin yabo ne, kuma zai taimaka wajen samun hadin kai a mashigar tekun yankin kasashen da ake fama da takalar fada, ganin yadda kasashen na Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu suka amince a hukumance su zauna don tattaunawa ranar Talata ta makon gobe, matakin da ke zama na farko a tsukin shekaru sama da biyu. A cewar Shugaba Trump dai wannan wani  abu ne da za a tsammaci sakamako mai kyau daga gare shi kamar yadda a nan ma Yoon Young-Chan babban sakaren hulda da jama'a na shugaban kasar Koriya ta Kudu ya fada.

Shugaban Amirka Donald Trump
Shugaban Amirka Donald TrumpHoto: Apicture-alliance/AP Photo/C. Kaster

Ana dai kallon duk wani shiri na tattaunawa tsakanin kasashen biyu a matsayin abu mai muhimmanci a kokarin samar da zaman lafiya tsakanin kasashen, sai dai wasu masharhanta na ganin Koriya ta Arewa na son amfani da damar wajen raba kan mahukunatan Seoul da na Washington. Haka nan kuma ta rage matsin lamba da kasar ke samu tsakanin kasa da kasa, da ma neman sassauci kan tarin takunkumi da aka kakaba wa kasar.