Shirin taron kasashe shida akan nuclearn Koriya ta arewa
November 27, 2006Talla
Jakadun kasashen Amurka dana Koriya ta kudu sun isa birnin Beijing din kasar Sin ,domin shirya tattaunawar kasashe shida,adangane da kawo karshen matsalar shirin nuclean kasar Koriya ta arewa,da akesaran gabatarwa a wata mai kamawa.Bayan gwajin makamin nucleanta na karkashin kasa a ranar 9 ga watan okt daya gabata nedai,koriya ta arewan ta amince da sake komawa teburin tattaunawar,batu daya kawo Allah wadai dasga kasashen duniya ,da bukatar kakaba mata takunkumi da amincewar mdd.Tattaunawar kasashe shidan dai ya hadar da koriyoyin biyu,da Amurka da Japan da Rasha,sai kuma ita kasar Sin mai masaukin baki.