A cikin shirin za a ji a wani mataki na kara tabbatar da dorewar zaman Lafiya a dukkanin kananan hukumomi 23 da ke a fadin jihar kadunan Najeriya, Kafafen watsa labarai da masu wasannin kwaikwayo da na barkwanci a na Jihar sun dukufa wajen kawo tasu gudunmawa ga hadin kan 'yan kasa da samar da zaman lafiya.