Shirin ya kunshi labaran duniya da rahotannin da suka hada da cece-kucen da 'yan Najeriya ke yi a kan zuwan likitocin China kasar don maganin Covid-19. Akwai rahoto kan halin da kasashen duniya ke ciki a kan annobar Coronavirus da kuma rahoto kan abin da likitocin Nijar ke cewa game da yadda ake samun mutuwar masu Corona a kasar.