An gaza samun hanyoyin magance rikicin Kamaru
May 29, 2019Makonni biyu da suka gabata Firaministan kasar ta Kamaru Dion Ngute ya yi tafiya zuwa yankin masu amfani da Turancin Inglishi na kasar ta Kamaru inda ya bai wa al'ummar yankin albishir na shirin bude zaman tattaunawa da zai hada illahirin bangarorin al'ummar kasar da nufin warware rikicin da ya hada gwamnatin da wasu al'ummonin yankin na Anglophone inda ta kai wasu ga daukar makamai da nufin aware.
Lamarin da ya yi sanadiyyar rasa rayuka da dama da kuma dukiyoyi da ma kuma tabarbarar da yanayin zamantakewa da rayuwa baki daya a yankin. To sai dai har ya zuwa yanzu shiru kake ji tamkar an shuka dura babu wata rana ko wurin da zaman tattaunawar zai gudana da gwamnatin Kamarun ta tsayar. To amma duk da haka Herve Emmanuel Nkom wani kusa mamba a kwamitin zartarwa na jam'iyya mai mulki ya ce suna cike da kyakkyawan fata.
A yankin na Anglophone na kasar ta Kamaru in baya ga masu ra'ayin aware, kusan illahirin al'ummomin yanki ne ke cike da fata na ganin an bude wannan zaman tattaunawa. Achu Nugute Tabe daya daga cikin 'yan yankin masu magana da Turancin Inglishi a kasar ta Kamaru da kuma ya nakalci harshen Faransanci rangadadam, na ganin wannan zama na iya kasancewa wata dama ta ganin an mika mulki ga wani dan yankin na Anglophone da kawo karshen rikicin baki daya.
Yanzu haka dai shugabannin 'yan siyasar kasar ta Kamaru da dama ne ke cewa har ya zuwa yanzu ba wanda ya taba tuntubarsu kan wannan batu ko kuma gayyatarsu halartar wannan zama. Sannan wani babban kalubalen da ke tattare da maganar ko da an tashi zaman tattaunawar, shi ne na sanin kowanne dan asalin kasar ta Kamaru ne ya dace ya jagoranci zaman ko kuma wani ya kamata a dauko daga waje.