Shirye-shiryen sake zaɓe a Jihar Agadez
March 22, 2011Talla
A janhuriyar Nijar mahawara ta kuno kai tsakannin Masana illimin doka akan maganar zaɓen 'yan Majalisun dokoki da za a sake gudanarwa a cikin jihar Agadez da ke a yankin arewaci na ƙasar.
Hakan kuwa ya biyo bayan kura kuran da kotun tsarin mulkin ta dago kan cewar wasu yan takara jam'iyyar na PNDS tarayya sun yi amfani da takardu na gogi a zaben farko
Ana sa ran dai shugaban jam'iyyar MNSD Nasara Seyni Omar da Mahaman Ousman shugaban jam'iyyar CDS rahama wanda basu da Kujeru a sabuwar Majalisar dokokin za su sake tsayawa takara a zaɓen na cike gurbi. Wakilimmu Gazali Abdou Tasawa ya aiko mana da rahoto dangane da wannan mahawara da ke gudana a Janhuriyar ta Nijar.
Edita: Zainab Mohammed Abubakar