1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bazoum ya yi tayin magance matsalar bakin haure

Ramatu Garba Baba
December 3, 2022

Shugaba Mohammed Bazoum ya nemi a shata yarjejeniyar daukar ma'aikata daga kasashen Afirka zuwa Turai don magance matsalar kwararar baki ta barauniyar hanya.

https://p.dw.com/p/4KQjH
Shugaba Mohamed BazoumHoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Shugaba Mohamed Bazoum ya ce, lokaci ya yi da shugabanin kasashen Turai dana Afirka za su zauna tare domin lalubo hanyar magance dadaddiyar matsalar kwararar bakin haure zuwa nahiyar Turai, Bazoum ya shawarci a shata yarjejeniya iyakance yawan ma'aikata da Turan ke bukata, yana mai cewa, yin hakan zai taimaka a warware matsalar tururuwar da bakin haure ke yi a duk shekara suna jefa rayuwarsu cikin hadari.

Shugaba Bazoum ya bayar da misali da kasashe kamar Faransa da Spain da Italiya da ke da bukatar ma'aikata a masana'antunsu, wanda idan an tantance adadin da suke bukata, za a iya cimma matsaya a tsakanin kasashen da takwarorinsu na Afirka na tura wadanda suka cancanta yin aiki a masana'antun na Turai.

Shugaban na Nijar ya yi wannan tayin ne a yayin wata ganawa da ya yi da takwaransa na Italiya Sergio Mattarella a ziyarar da ya kai a kasar Italiya bayan wata fira da ya yi da wata jarida da ake wallafawa a kasar.

A kowacce shekara ana samun dubban 'yan Afirka da ke jefa rayuwarsu cikin hadari a bi ta ruwa ko sahara da zummar zuwa Turai don samun ingantacciyar rayuwa, Nijar na daga cikin barauniyar hanya da matasan Afirka ke bi don zuwa Turan.