1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaba Embalo ba zai nemi wa'adi na biyu ba

Mouhamadou Awal Balarabe
September 19, 2024

Shugaba Umaro Embalo na kasar Guinea-Bissau ya ba da mamaki a lokacin da ya sanar da cewa ba zai sake tsayawa takara don neman wa'adi na biyu na mulki ba duk da damar da kundin tsarin mulki ya bashi.

https://p.dw.com/p/4krjE
Guinea-Bissau | Umaro Sissoco Embaló | Archivbild
Hoto: Phill Magakoe/AFP

Ba watsi da damar sake tsayawa takara a karo na biyu da shugaban kasar Guinea-Bissau ya yi ba ne ya fi ba da mamaki, amma furuncin Umaro Sissoco Embalo na cewa babu wani abokin hamayyarsa ta siyasa da zai gaji kujerar mulki, imma Domingos Simoes Pereira ko Braima Camara ko kuma Nuno Nabiam ba. Hasali ma dai, Domingos Simoes Pereira shi ne ke shugabantar jam'iyyar PAIGC da ta fara mulki bayan samun 'yancin kasar ne madugun adawa.  Kuma shi kansa Embalo tsohon dan wannan jam'iyyar ne kuma har ma ya taba zama firayiminista a gwamnatin da ta kafa a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2018. Daga bisani ya shiga cikin gungun 'yan adawa da suka kafa jam'iyyar MDEM G15. Amma a yanzu Shugaba Sissoco Embalo ya sa kafar wando guda da jagororin wannan jam'iyya a yayin jawabin da ya yi wa 'yan jarida.

'Yan Jam'iyyar MADEM-G15 na Guinea-Bissau
'Yan Jam'iyyar MADEM-G15 na Guinea-BissauHoto: Djariatú Baldé/DW

"A cikin jirgin sama, a kan hanyar dawowa daga taron kolin Sin da Afirka, matata ta ce da ni, Shugaba, bai kamata ka sake tsayawa takara karo na biyu ba. Sai na tambaye ta dalili, sai ta ce min na cancanci abu mai kyau da ya dara wa mulki. Ni kuma lokacin da na dawo sai na gaya mata cewar ba zan sake tsayawa takara ba. Amma, na so in bayyana abu daya a nan: Domingos Simoes Pereira ko Braima Camara ko Nuno Nabiam ba za su gaje ni ba. Guinea-Bissau na cancantar samun wasu shugannin fiye da wadannan."

Sai dai a babban zaben da ya gabata, PAIGC ta samu rinjaye a majalisar dokokin, amma Shugaba Sissoco Embalo ya ki nada Simoes Pereira a matsayin firaminista. Maimakon haka ma, ya rusa majalisar dokokin Guinea Bisau kuma ya fara tafiyar da harkokin mulkin kasar ba tare da bangaren majalisar dokoki ba. Sannan madugun adawa Simoes Pereira ya fice daga Guinea-Bissau inda ya nemi mafaka a Portugal da ta yi wa kasarsu mulkin mallaka. Sai dai ofishin mai shigar da kara na Guinea-Bissau na neman a dawo da shi gida domin a yi masa tambayoyi game da batun cin hanci da rashawa, zargin da Pereira ya musanta kuma ya yi ikirarin cewar bita da kullin siyasa ce. Daga bisani ne wata kotu ta yi watsi da karar a shekarar 2018, lamarin da ya bai wa dan adawa Simoes Pereira damar komawa Guinea-Bissau. Sai dai ya ki cewa uffan kan matakin Shugaba Embalo na yin watsi da wa'adin mulki na biyu.

Magoya bayan Jam'iyyar MADEM-G15 ta Guinea-Bissau
Magoya bayan Jam'iyyar MADEM-G15 ta Guinea-BissauHoto: Djariatú Baldé/DW

"Ba zan yi tsokaci kan matakin da Sissoco ya dauka na kin sake tsayawa takara ba, wannan shawara ce ta shugaban kasa shi kadai. Amma ina so in nuna cewa a tsarin dimukuradiyya, dan siyasa zai iya zama shugaban kasa ne kawai idan ya bi tsarin doka da oda, idan kuma yana shirye wajen mutunta ra'ayoyi daban-daban a kasar."

Shi kuwa Braima Camara, wanda ke shugabantar jam'iyyar MDEM G15 mai mulki, ya zargi shugaban Guinea-Bissau da rashin mutunta tsarin dimukuradiyya, lamarin da ya sa Shugaba Embalo ya yi kokarin mayar da shi saniyar ware a jam'iyyar, lamarin da ya sa jam’iyyar mai mulki ta rabu gida biyu. A nasa bangaren, Nuno Nabiam, shugaban karamar jam'iyyar APU-PDGB, wanda ya kasance firayiminista a karkashin Embalo daga 2020 zuwa 2023, ya zargi Shugaba Embalo da gudanar da mulkin kama-karya. Hasali ma, rikici tsakaninsu ya kai ga Nabiam yin hijira a Portugal na wani dan lokaci, amma a yanzu ya bayyana rashin neman wa'adi na biyu na Shugaban Guinea-Bissau a matsayin yunkuri na neman kawar da hankali a kan matsalar muggan kwayoyi da aka kama a filin jirgin saman birnin Bissau.

Guinea-Bissau | Matasa maza da mata na PAI Terra Ranka
Hoto: Iancuba Danso/DW

Ko shi ma Luis Petit, wani manazarcin siyasa mai zaman kansa, yana daukar sanarwar Embalo na rashin sake tsayawa takara a matsayin dabara ta siyasa don raunana abokan hamayyarsa saboda yana da yawan saba alkawari. 

"Wannan magana ce mai matukar ban mamaki a gare mu baki daya, domin kafin wannan balaguron kasar waje ya yi ta maganar sake zabensa a karo na biyu. Sai mu jira mu gani ko da gaske ne shugaban kasar na nufin aiwatar da abin da ya ce, domin ya saba alkawari amma ya aikata akasin haka."

Guinea-Bissau na tunkarar manyan kalubalen siyasa, inda a ranar 24 ga Nuwamban 2024 za a gudanar da zabukan 'yan majalisar dokoki, amma har yanzu ba a fitar da jadawlin zaben shugaban kasa ba. Alhali bisa ga dokar kasar, ya kamata a gudanar da zaben shugaban kasa a cikin wannan shekara ta 2024, amma Shugaba Embalo ya ce ba za a iya gudanar da shi kafin 2025 ba. A halin yanzu dai, al'amuran siyasa a kasar Guinea-Bissau na ci gaba da tabarbarewa, kuma ba a san makomar dimukuradiyyarta ba. Hasali ma, kalaman da Embalo ya yi masu cin karo da juna da kuma rigingimun siyasa suna jawo ayar tambaya kan ko Guinea-Bissau na kan hanyar samun kwanciyar hankali ko kuma za a kara samun tashin hankali a siyasance.