Shugaba Khadafi ya shawarci girka gwamnatin haɗin kan Afrika
July 3, 2007Saban shugaban ƙungiyar gamayya turai, bugu da ƙari Praministan Portugal, Jose Socrates, ya gabatar da wani mahimmin jawabi, a taron ƙoli karo na 9, na ƙungiyar taraya Afrika, da aka rufe yau a birnin Accra na ƙasar Ghana.
Socrates ya alƙawarta gudanar da kwaskawarima ga mu´amila tsakanin Afrika da ƙasashen turai.
Za shi bayyana mayan matakan da kwaskwarimar ta tanada a taron da zai haɗa ɓangarorin 2, a birnin Lisbonne, na Portugal daga 8 zuwa 9 ga watan desember.
Saidai tunni, ya ce batutuwan kare haƙƙoƙin bani adama, yaƙi da talauci, da kuma kwararar baƙin haure, za su kasance ƙashin bayan sabuwar mu´amila tsakanin Afrika da EU.
A jawabin da yayi albarkacin rufe wannan taro, shugaban ƙasar Lybia, Muhhamad Khaddafi, ya bada shawara girka haɗɗaɗiyar gwamnatin nahiyar Afrika, ranar 1 ga wata Janairu na shekara ta 2008.
Wannan gwamnati zata ƙunshi ministoci 15, da su ka haɗa da ministan tsaro , da na harakokin waje, da kuma ministan kasuwanci da ƙasashen ƙetare.
Shugaba Khaddafi, ya bukaci ƙungiyar AU,ta girka komitin shugabanin ƙasashe 5, wanda za su ci gaba da tunani a game da yiwuwar kafa gwamnatin Afrika.