1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Shugaba Ruto na Kenya ya nemi ganawa da masu zanga-zanga

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 23, 2024

Shugaban na jinjinawa matasan bisa nuna 'yancin da dimukuradiyya ta ba su na bayyana ra'ayinsu

https://p.dw.com/p/4hPFX
Hoto: James Wakibia/ZUMA PRESS/picture alliance

Shugaba William Ruto na Kenya ya ce a shirye yake don ganawa da dubban matasan da ke zanga-zangar da ta tayar da hankalin kasar suna nuna tirjiya ga matakin da ya dauka na kara kudaden haraji ga 'yan kasa.

Karin bayani:Gangamin tsadar rayuwa a Kenya ya yi nasara

Sanarwar da mai magana da yawun fadar shugaban kasar Hussein Mohamed ya fitar a shafinsa na X, a Lahadin nan, ta rawaito shugaban na jinjinawa matasan bisa nuna 'yancin da dimukuradiyya ta ba su na bayyana ra'ayinsu, yanzu abin da ya rage shi ne tattaunawa da juna don sanin bukatunsu, domin daukar matakin da ya dace a kai.

Karin bayani:Masu zanga-zanga kan tsadar rayuwa sun sake fitowa a Kenya

To sai dai matasan ba su ce komai ba game da wannan martani na shugaban kasa, bayan da suka yi kiran gudanar da yajin aiki a fadin kasa, daga ranar Talata mai zuwa, 25 ga wannan wata na Yuni da muke ciki.

Zanga-zangar dai ta yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu a Nairobi babban birnin kasar, inda wasu da dama kuma suka samu raunuka, sakamkon arangama da 'yan sanda dake harba musu hayaki mai sa hawaye da kuma bindiga.