1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Ziyarar Shugaba Scholz a Isra'ila

Zainab Mohammed Abubakar
October 17, 2023

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz na ziyara a Isra'ila domin nuna goyon bayansa ga mahukuntan kasar bayan harin da Hamas ta kaddamar daga zirin Gaza.

https://p.dw.com/p/4Xdlq
Deutschland Berlin | Regierungserklärung zur Lage in Israel | Olaf Scholz
Hoto: Bernd von Jutrczenka/dpa/picture alliance

A yayin da sojojin Isra'ila ke ci gaba da yi wa zirin Gazakawanwa, Scholz na zama shugaban gwamnati na farko da ya tafi Isra'ila bayan rikicin da ya barke a yankin Gabas ta Tsakiya sama da mako guda.

Ana sa ran zai tattauna da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin Tel Aviv kafin ya wuce Masar domin ganawa da shugaba Abdel Fattah al-Sissi.

Shugaban gwamnatin Jamusya ce yana son tattauna halin da ake ciki a yankin da ake yaki, da kuma yadda za a kaucewa ta'azzarar rikicin. Wani muhimmin batu kuma shi ne, mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su, daga cikinsu akwai 'yan kasar Jamus da dama.