Shugaba Trump na fuskantar guguwar siyasa a Amirka
May 11, 2017Talla
A wannan Alhamis din ce (11.05.2017) dai Darectan riko na hukumar ta FBI Andrew McCabe, zai fuskanci babban kwamitin nan na 'yan majalisar ta Amirka masu kula da fannin tattara bayannai domin bada ba'asi, kuma daya daga cikin kwamitocin da ke bincike kan tuhumar da ake yi wa kasar Rasha da yin kutse kan zaben na Amirka. Hakan ta sanya wasu 'yan majalisa guda biyu daga bangarorin biyu, ke aza ayar tambaya kan dalillan cire Darectan na hukumar FBI a daidai wannan lokaci, kuma tuni 'yan adawa suka soma zargin Shugaba Trump da neman yin kafar ungulu kan binciken da ka iya shafa masa kashin kaji. Sai dai kuma Shugaba Trump din ya ce matakin ba shi da wata alaka da binciken da ake yi.