1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Afghanistan ya fice daga kasar

August 15, 2021

Rahotanni daga Kabul babban birnin kasar Afghanistan na nuni da cewa wasu jami'an kungiyar Taliban sun ce za a samar da gwamnatin rikon kwarya a kasar.

https://p.dw.com/p/3z1WA
Afghanistan Präsident Ashraf Ghani
Hoto: Sajjad Hussain/AFP

Kungiyar Taliban na jiran a mika mata ragamar mulkin Afghanistan. Tuni dai shugaba Ashraf Ghani ya fice daga kasar tun bayan da mayakan Taliban suka sami nasarar kutsawa birnin Kabul, suna masu ikrarin sake karbar ikon kasar bayan shekaru 20 da sojojin kasa da kasa suka kwace mulki a hannunsu.

Kawo yanzu dai ba a san inda shugaban kasar yake ba.

Mukadashin ministan harkokin cikin gida na kasar Abdul Sattar Miryakawal ya ce za a mika ragamar mulkin kasar ga gwamnatin rikon kwarya.