Shugaban Amirka ya isa birnin Addis Ababa na Habasha
July 27, 2015Talla
Shugaba barack Obama na kasar Amirka yana isa kasar Habasha a mataki na biyu na ziyara a kasashen Afirka, inda ya fara da kasar Kenya da ke zama mahaifar mahaifinsa.
Shugaba ya samu kekkyawar tarba lokacin da ya isa birnin Addis Ababa fadar gwamnatin kasar Habasha, inda birnin ya sha ado da hotunan Obama tare da sakonni yi masa maraba.
Shugaba Obama zai tattauna da Firaministan Habasha da sauran manyan jami'an gwamnati tare da jawabi a helkwatar kungiyar Tarayyar Afirka.