Shugaban bankin duniya ya ajiye aiki
January 8, 2019Babban bankin duniya ya tabbatar da murabus din shugabansa Jim Yong Kim shekaru uku gabannin wa'adin shugabancinsa a shekarar 2022. Kim ya nuna gamsuwa da kasancewa shugaban bankin duniya na tsawon shekaru, ya ce ajiya aikin zai ba shi damar maida hankali kan harkokin kasuwanci da zuba jari a kasashe masu tasowa.
A watan Yulin shekara ta 2017 ne Jim Yong Kim ya fara jan ragamar shugabancin bankin duniya karo na biyu bayan da ya gaji tsohon shugaban bankin Robert Zoellick a 2012 karkashin shugabancin tsohon Shugaban Amirka Barack Obama.
A ranar 1 ga watan Fabrairun shekarar 2019 ne wa'adin Kim zai kawo karshe a hukumance, yayin da Kristalina Georgieva za ta kasance mukaddashiyar shugaba. Shugaban Amirka Donald Donald Trump na da damar sake zaban wanda zai shugabancin bankin duniya nan gaba.