Macron na ziyarar farko a Jamus
May 15, 2017Batun huldar dangantakar kasashen biyu musamman a game da manufofinsu kan kungiyar Tarayyar Turai ta EU, na daga cikin muhimman batutuwan da Shugaba Macron ya tattauna da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel a lokacin ganawar da suka yi a birnin Berlin fadar gwamnatin kasar ta Jamus:
Kamar dai yadda shugaba Hollande da ya gaba ce shi ya yi shekaru biyar da suka gabta, shi ma dai sabon shugaban na Faransa Macron ya soma ziyararsa ta farko a kasar Jamus, inda ya ya samu babban tarbo daga Shugabar Gwamnatin ta Jamus Angela Merkel wacce ke cike da kwarin gwiwa dangane da makomar huldar dangantaka da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma Tarayyar Turai. Sai dai a wannan ziyara babu wani batun jarjejeniyoyi da ake jira, amma kuma ana ganin shugabannin biyu ka iya duba wasu mahimman batutuwan da za su sa wa gaba.