Shugaban hukumar IAEA zai ziyarci Iran
August 22, 2020Talla
Wannan ziyara ita ce ta farko da shugaban hukumar Rafael Mariano Grossi zai kai kasar ta Iran tun bayan da ya fara jagoantar hukumar a watan Disambar shekarar da muka yi bankwana da ita.
Ziyarar na zuwa ne daidai lokacin da ake cigaba da samun tada jijiyar wuya tsakanin kasashen Turai da Amirka kan dangantaka da Iran din saboda shirin nukiliyarta, wadda kasashe da yawa musamman ma Amirka ke cewar tana yinsa ne don kera makamin kare dangi, sai dai Iran din ta sha musantawa inda ta ce shirin nata na zaman lafiya ne don kuwa tana yinsa ne don samar da makamashi.