Shugaban hukumar zaben Gambiya ya tsere
January 4, 2017Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP wanda ya ruwaito labarin, ya ambato wani daga cikin iyalan shugaban hukumar zaben da amma bai so a bayyana sunansa ba, na cewa Alieu Momar Njie ya gudu ne shi da wasu membabobin hukumar zaben, bayan da suka samu labarin mahukuntan kasar ta Gambiya na shirya masu wata makarkashiya.
Kawo yanzu dai ba a da wani cikakken bayani kan lokacin da shugaban hukumar zaben ya gudu dama kuma irin barazanar da ya fuskanta da ta sanya shi tserewar.
Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ta Gambiya ta shiga wani rudanin siyasa, tun bayan da Shugaba Yahya Jammeh wanda ya amince da farko da shan kayi a zaben shugaban kasar da ya gudana a kasar, ya canza ra'ayi daga bisani a bisa zargin hukumar zaben kasar da rashin yin adalci a zaben da ya bayyana madugun 'yan adawar kasar Adama Barrow a matsayin wanda ya lashe zaben.