Shugaban Iran na farko ya rasu
October 9, 2021Talla
Shugaban kasar Iran na farko bayan juyin juya halin Musulunci a shekarar 1979, Abolhassan Banisadr ya rasu a wani asibiti a birnin Paris na kasar Faransa bayan doguwar jinya.
Marigayi Banisadr ya rasu yana da shekaru 88 a duniya, ya kasance dan gwagwarmaya tun yana da shekaru 17, ya taba zama ministan tattalin arziki da harkokin waje.
Mariyagayin ya zama shugaban kasa a watan Janairun 1980, sai dai majalisar dokokin Iran ta raba shi da kujerar shugabncin kasar a 1981 bayan ya yi adawa da marigayi jagoran addini Ayatollah Ruhollah Khomeini, matakin da ya tilasta shi yin hijira a Faransa.