Shugaban kasar Jamus na ziyarar aiki a Poland
June 17, 2021Talla
Biyo bayan kwashe shekaru talatin da kulla wata alakar diplomasiya ta kut da kut tsakanin kasashen Jamus da Poland shugabannin kasashen guda biyu sun yi wata ganawa ta musamman a yau din nan.
A ziyarar da ya kai a birnin Warsaw na kasar Poland, shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da takwaransa Andrzej Duda sun tattauna batutuwan da suka shafi makomar kungiyar Tarayyar Turai da kuma halin da ake ciki a Ukirain da Belarus albarkacin wannan rana.
Sai dai tun gabanin haduwar ta mahukuntan na Berlin da Warsaw ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya tabbatar da cewa kasashen guda biyu za su cigaba da aiki kafada da kafada da juna.