Shugaban kasar Kenya ya rusa gwamnatin sa
November 23, 2005Shugaban kasar Kenya Maw Kibaki, ya russa gwamnatin sa, bayan mummunan kayin da ya sha, a zaben jin ra´ayi jama´a, a game da kundin tsarin mulkin kasa, da a ka gudanar ranar litinin da ta wuce.
A jawabi da yayi ta kafofin sadarwa, ya nunar da cewa, bayan abunda ya wakana, ya zama wajibi a gare sa, ya yi garambawul ga gwamnati kasancewar an samu rabuwar kanu tsakanin ministoci lokacin yakin neman zabe.
A yayin da wasu su ka yi kampe ta rashin amicewa da kundin tsarin mulkin, wasun kuwa sun bukaci a amince da shi.
Shugaban ya sannar da cewa, nan da sati 2 masu zuwa, zai kafa wata sabuwar gwamnati, da za ta dukkufa ga ayyukan ci gaban kasa.
Masharahanta na hasashen cewa, a cikin sabuwar gwamnatin da za a girka sahugaban zai fidda dukkan ministocin da su ka kiri al´umma da ta kauracewa kundin tsarin mulkin.