Shugaban kasar Namibiya Hage Geingob ya mutu
February 4, 2024Shugaban kasar Namibiya ya mutu da sanhin safiyar Lahadi 04.02.2024 a wani asibiti da ke Windhoek babban birnin kasar inda da aka kwantar da shi domin jinyar cutar daji ko kuma cancer.
Majigayi Hage Geingob ya dare kan mulki Namibiya a karon faron a shekarar 2014 sannan kuma ya kara samun wani wa'adin mulki na biyu a shekarar 2019, kafin ya mutuwa ta dauke sa yana dan shekaru 83 a duniya.
A lokacin da yake raye Hage Geingob wanda aka haifa a shekarar 1941 a Arewacin kasar Namibiya, ya kasance daya daga cikin 'yan gwagwarmayar da suka jagoranci samun 'yancin kan kasar a shekarar 1990, sannan kuma za a iya tunawa da fafutikar da ya yi ta yaki da gwamnatin masu nuna wariyar launin fata ta Afrika ta Kudu.
A fagen siyasar wannan zamani Hage Geingob na daga cikin wadanda suka goya wa Afrika ta Kudu baya a lokacin da ta maka Isra'ila a kutun duniya kan rikicin zirin Gaza na yankin Falasdinu.
Kafin ya zama shugaban kasa, Geingob ya rike mukamin Firaminista na tsawon shekaru 12 bayan dawowarsa gida daga Amurka inda ya yi zaman gudun hijira.
Tun bayan sanar da mutuwarsa, shugabanni kasashe na ta aike wa kasar sakonnin ta'aziyya kan wannan rashi na daya daga cikin dattijawan shugabanni masu hangen nesa da kuma karfin fada a ji a Nahiyar Afrika.