Shugaban Komitin Koli na 'yan adawar Siriya yayi murabus.
March 24, 2013Shugaban 'yan adawar Siriya da ke fafutukar kawar da shugaban kasar Bashar al-Assad daga gadon mulki wato Ahmed Moaz al-Khatib ya bada sanarwar barin aiki a wannan Lahadin.
A wani sako da ya fidda ta shafinsa na Facebook, Mr. al-Khatib ya ce ya yi murabus ne saboda yadda abubuwa su ke tafiya a kungiyar tawaye ta "Free Syrian Army", wanda ya ce ya saba da irin yadda ya kamata abubuwa su ta fi a yunkurin da su ke na kaiwa ga karbe iko da kasar, kana duniya ta zuba idanu ta kallo ana ta yi musu kisan kiyashi.
Murabus din na al-Khatib na zuwa ne 'yan kwanaki kalilan da zaben Ghassan Hitto a matsayin Firaministan 'yan tawayen wanda shi al-Khatib ke adawa da shi domin a cewar sa an kakaba musu shi ba da son ran su ba.
Wannan hali da aka shiga dai yanzu haka ya sanya kungiyar 'yan tawayen wadda dama ke fama da rabuwar kai shiga wani hali na rashin tabbas a yakin da su ke da gwamnatin Assad.
Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Yahouza Sadisou Madobi