Shugaban Myanmar zai tattauna da Barack Obama
May 20, 2013Talla
Shugaban ƙasar Thein Sein zai kai ziyara ne wace a cikin sama da shekaru 40 babu wani shugaban ƙasar na Myanmar da ya taɓa kai irinta a Amurika.
Tun bayan wadda jagoran mulkin soja na ƙasar janar Newin ya kai a shekaru 1966 zamanin mulkin Lyndon johnson na Amurikan. Wannan ziyara ta biyo bayan sauye sauye da sojojin suka ƙaɗɗamar na kafa wata gwamnatin farar hula tun a shekarun 2011 tare da shirya zaɓuɓɓuka. Thein Sein fira minitan na sojojin da ya zama shugaban ƙasa a shekarun 2011 ya taka muhimmiyar rawa wajan sako pursunan siyasa na ƙasar a ciki hada jagorar ' yan addawar Aung San Suu Kyi.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman