1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Trump ya halarci taron Nato a karon farko

Gazali Abdou Tasawa
May 25, 2017

A wannan Alhamis ce a birnin Brussels ake bude zaman taron kungiyar kawancan tsaron ta NATO wanda a karon farko Shugaba Trump na Amirka zai halarta.

https://p.dw.com/p/2dYmI

A wannan Alhamis ce a birnin Brussels ake bude zaman taron kungiyar kawancan tsaron kasa da kasa ta NATO ko Otan inda a karo na farko Shugaba Donald Trump na Amirka zai tattauna da shugabannin kasashen Turai kan batun kungiyar ta NATO wacce a baya a bayyana ta a matsayin maras amfani. 

Shugaba Trump zai halarci bikin kaddamar da sabuwar cibiyar kungiyar ta Nato inda zai gabatar da wani kiran birgi na ginin tsohuwar cibiyar kasuwanci ta World Trad Center da aka kai wa hari ta'addanci a ranar 11 ga watan Satumbar 2001, a yayin da Shugabar Gwamnatin Jamus Angela Merkel  za ta gabatar daga nata bangare wani kiran birgin tsohuwar katangar Berlin, dukkaninsu da nufin nuna goyon bayansu ga yaki da ta'addanci. 

Kasashen Turan dai na fatan a jawabinsa Shugaba Trump zai jaddada goyon bayansa ga yarjejeniyar Washington wacce ta tanadi kawo dauki ga duk wata kasa mamba a Kungiyar ta NATO da za ta fuskanci hari daga wata kasa ta daban.