1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanni na halartar taron tsaro a Munich

Yusuf Bala Nayaya
February 16, 2018

Gwamman shugabanni na duniya da manyan jami'an tsaro da na diflomasiya sun tattaru a kudancin Jamus don halartar taro na tsaro mai tasiri.

https://p.dw.com/p/2so2X
MSC 2018 Logo
Hoto: picture-alliance/NurPhoto/A. Pohl

Taron tsaron na zuwa ne a daidai lokacin da a ke ci gaba da tada jijiyoyin wuya tsakanin Amirka da sauran kasashe na kungiyar tsaro ta NATO saboda rikici da ke faruwa a Siriya da Ukraine.

Sakataren tsaron Amirka James Mattis shi ke jan ragamar tawagar Amirka zuwa wannan taron tsaro na Munich. An dai tanadi 'yan sanda da dama don tabbatar da tsaro a wannan taro da a ke sa ran halartar Firaminista Theresa May ta Birtaniya da Benjamin Netanyahu na Isra'ila da Firaministan Iraki Haider al-Abadi da Shugaba Petro Poroshenko na Ukraine da ministocin harkokin waje na kasashen Rasha da Iran da Turkiya.

Wolfgang Ischinger shugaban taron tsaron na Munich ya ce yana da kyakkyawan fata ga taron.