1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin addini sun bukaci magance Boko Haram nan take

Ibrahima YakubuNovember 12, 2014

Kungiyar Jama'atul Nasarul Islam ta koka matuka gami da yadda gwamnati ta gaza wajan samar wa sojojin Najeriya kayan yaki na zamani don kawar tashin hankali a kasar

https://p.dw.com/p/1Dm0w
Nigeria Sa'ad Abubakar III. Sultan von Sokoto
Hoto: Sultan's Office

A wani taron gaggawa da ta ta yi yau Laraba, ta bukaci gwamnatin Tarayyar Najeriya da ta hanzarta kawo karshen aiyyukan 'yan Boko Haram da ke kara tsananta da karuwar tabarbarewar harkokin tsaro, wanda ke addabar al'umman kasar.

Wani babban batu kuma da kungiyar ta tattauna shi ne na tabbatar da ganin cewar gwamnatin ta wadata isassun kayayyakin yaki na zamani da suka dace ga manya da kananan dakarun sojojin kasar, wadanda a yanzu haka suke fagen daga, domin kara masu kwarin gwiwa, ta yadda za su magance wannan al'amari.

Nigerianische Truppen bereiten sich auf Einsatz in Mali vor
Hoto: Reuters

Dr Khalid Aliyu Abubakar shi ne dai sakatare janar na kungiyar ta Jama'atul Nasrul Islam na kasa, da ya bayyana wasu daga cikin matakan da suka dauka na bukatar don tabbatar da dorewar zaman lafiya.

"A dukkanin wadannan hare-haren da ake kai wa, Musulmai da kiristoci duk suna mutawa, to amma da yake lamari ya fi faruwa a inda musulmai ke da rinjaye, musulmai ne suka fi mutuwa fiye da yawan kiristoci. Muna san ganin gwamnati ta dawo akan akin da aka santa da shi, wanda shi ne na kare rayuka da tattalin arzikin al'umma, kuma tabbatar da ganin cewa, an bai wa jami'an tsaro makaman da suka dace na zamani. Domin tinkarar masu tayar da zaune tsaye da ke gudanar da aiyyukan da suka jibanci na tauye hakkkin bil Adama da ke gurgunta tattalin arzikin kasa"

A binciken da wasu kungiyoyi addini suka gudanar, sun nunar da cewa kimanin hare- hare guda takwas ne aka kai a wasu jihohin arewa tun shigowar wannan wata , lamarin da ya janyo mutuwar daruruwar al'umma da tursasa dubbai 'yan gudun hijira, da kuma yadda 'yan kungiyar ke ci-gaba da samun nasara da mamaye sabbin garuruwa suna maida su a karkashin mulkin su.