Shugabannin Afirka 10 da suka rasu a kan mulki
Ana rade-radin rashin lafiyar Shugaba Buhari na Najeriya da Shugaba Bouteflika na Aljeriya. Wannan ya tunatar da shugabanni 10 da suka mutu kan mulki cikin shekarun nan a Afirka.
1) Michael Sata, shugaban Zambiya (2014)
Michael Sata ke zama shugaba na baya-baya da ya mutu a bakin aiki. Ya rasu yana da shekaru 77 sakamakon cutar da ba a bayyana ba a asibitin Birtaniya ranar 28 ga watan Oktoba 2014. Bayan zabensa a 2011, aka fara yada gita-gita bisa halin lafiyarsa a Zambiya. Rashin ganin sa lokacin taruka ya fara janyo damuwa kan halin da yake ciki, duk da mai magana da yawun gwamnati ya ce yana da koshin lafiya.
2) Meles Zenawi, firaministan Habasha (2012)
Meles Zenawi ya rasu a watan Agusta 2012 a Beljiyam yana da shekaru 57 da haihuwa sakamakon cutar da ba a bayyana ba. Ya mulki Habasha na tsawon shekaru 21, a matsayin shugaban kasa daga 1991 zuwa 1995 da kuma firaminista 1995 zuwa 2012. Shi ya fito da tsarin jam'iyyu da dama a kasar, amma ya yi amfani da karfi wajen dakile boren Oromia da ke kan ka'ida a yankin arewacin Habasha.
3) John Atta Mills, shugaban Ghana (2012)
Har ila yau a 2012, John Atta Mills, shugaban Ghana, ya rasu a kasarsa sakamakon bugun zuciya da sankara na wuya yana da shekaru 68 da haihuwa. Ya lashe zaben shekara ta 2008 kuma ya yi mulki na tsawon shekaru uku kacal. A matsayin shugaban kasa, ya kaddamar da sauye-sauye masu tasiri kan tattalin arziki da zamantakewa abin da ya janyo masa daukaka a ciki da wajen kasar.
4) Bingu wa Mutharika, shugaban Malawi (2012)
Wani shugaban da ya rasu a 2012 shi ne Bingu wa Mutharika, shugaban Malawi. Ya yi fama da bugun zuciya a watan Afrilu sannan ya rasu bayan shekaru biyu yana da shekara 78 da haihuwa. A shekaru takwas na mulki ya samu nasara kan shirin bunkasa noma da samar da abinci. Mutuncinsa ya zube sakamakon zanga-zanga saboda shirin sayen jirgin sama na shugaban kasa a kan kimanin Euro milyan 13.
5) Malam Bacai Sanha, shugaban Guinea-Bissau (2012)
Shugaba na hudu da ya rasu a 2012 shi ne Malam Bacai Sanha, shugaban Guinea Bissau. Ya yi fama da ciwon suga inda ya mutu a birnin Paris na Faransa bayan mulkin shekaru hudu kuma ya na da shekaru 64 da haihuwa. Gaba daya lokacin mulkin yana yama da matsalolin rashin lafiya kullum yana asibiti.
6) Moammar Gadhafi, dan uwa shugaba kana jagoran juyin-juya hali na Libiya (2011)
Moammar Gadhafi ya gamu da kisan gilla wanda shi ya ayyana kansa a matsayin jagoran kan juyin-juya hali. 'Yan tawaye suka kashe shi yana da shekaru 69 cikin yanayi mai sarkakiya cikin Libiya, bayan mulkin shekaru 42. Ya kwaci iko a 1969 ta hanyar juyin mulki ga masarautar kasar, amma mulkinsa ya kawo karshe sakamakon juyin juya hali na kasashen Larabawa.
7) Umaru Musa Yar’Adua, shugaban Najeriya (2010)
Umaru Musa Yar’Adua, ya rasu a 2011 yana da shekaru 58 sanadiyar cuta mai nasaba da zuciya. Ya shafe shekaru uku kacal kan madafun iko. Lokacin yakin neman zabe ba kullum yake tafiye-tafiye ba kuma akwai rahotanni kan rashin lafiya. Bayan watan Afrilu 2007 lafiyar shugaba Yar'Adua ta kara tabarbarewa.
8) Joao Bernardo Vieira, shugaban Guinea Bissau (2009)
Joao Bernardo Vieira, shugaban Guinea Bissau ya yi masa kisan gilla a kasarsa a shekara ta 2009 yana da shekaru 69 da haihuwa. Ya mulki kasar a gaba daya na shekaru 31. A 1978 ya zama firaminista sannan ya kwace mulki a 1980 inda ya yi mulkin shekaru 19. ya sake dawowa a matsayin farar hula na karin shekaru hudu. A 2005 Vieira ya sake lashe zaben shugaban kasa.
9) Omar Bongo, shugaban Gabon (2009)
Cutar sankara ta yi awun gaba da Omar Bango a watan Yuni na 2009 a birnin Barcelona na Spain, bayan mulkin shekaru 42. Ya rasu yana da shekaru 72 daya daga cikin shugabanni mafiya dadewa a tarihi, kana wanda ya wawushe dukiyar kasa. Bongo yana da dukiya yayin da mutanen kasar ke rayuwa cikin talauci duk da arzikin da Gabon take da shi na samun kudaden man fetur.
10) Lansana Conte, shugaban Guinea (2008)
Bayan mulkin shekaru 24, Lansana Conte ya rasu samakon cutar da ba a bayyana ba yana da shekaru 74 da haihuwa. Ya dade yana fama da cutar siga gami da cuta mai nasaba da zuciya. Tun daga watan Afrilu na 1984 har lokacin da ya rasu a Disamba 2008, ya kasance shugaban Guinea na biyu. Duk da rashin lafiya da tafiya kasashen ketare domin neman magani ya lashe zabuka so uku.