Shugabannin Afirka guda 6, sun sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da raya ƙasa a birnin Nairobin ƙasar Kenya.
December 15, 2006Shugabannin Afirka guda 6, na yankin manyan tafkunan nan na gabashin Afirka, sun rattaba hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da raya ƙasa a wannan yankin, a wani bikin da aka gudanar yau a birnin Nairobi na ƙasar Kenya. Burin wannan yarjejeniyar dai, shi ne faɗaɗa yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali da ake samu a duk faɗin yankin gaba ɗaya.
Zaɓen da aka gudanar a Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango, da ƙasar Burundi da kuma bunƙasar tattalin arziki da ci gaban raya ƙasa da ake samu a ƙasar Rwanda, na ƙara kaɗa iskar fatar da ake yi na samun zamman lafiya mai ɗorewa a yankin manyan tafkunan, na nahiyar Afirka.
Da yake yi wa maneman labarai jawabi a birnin na Nairobi, bayan rattaba hannunsa kan yarjejeniyar, shugaban ƙasar Jumhuriyar Dimukraɗiyya Ta Kwango, Joseph Kabila, ya ce wannan bikin dai wato ƙololuwar wata tattaunawa mai wuya da aka yi ne, amma wadda a ƙarshe za ta bai wa duk al’umman yankin wata kyakyawar hanya ta inganta dimukraɗiyya, da kafa da gwamnati ta nagarta da kuma samun bunƙasa a duk fannonin halin rayuwa.
Sauran shugabannin ƙasashen da suka halarci taron sun haɗa ne da na Kenya, da Uganda, da Burundi, da Zambiya. Firamiyan ƙasar Rwanda, tare da manyan jami’an Majalisar Ɗinkin Duniya da na Ƙungiyar Tarayyar ASfirka, wato AU, su ma sun halarci taron. Wakilan gwamnatocin ƙasashen Angola, da Jumhuriyar Afirka Ta Tsakiya, da Jumhuriyar Kwango da kuma Sudan ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a madadin shugabannin ƙasashensu.