Ci gaba da kai ruwa rana kan rikicin bashin Girka
July 1, 2015Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nanata matsayinta game da sabbin tattaunawar da za a yi da kasar Girka, tana mai cewa za a iya sake komawa kan teburin tattaunawar ne bayan kuri'ar raba gardama ta ranar Lahadi mai zuwa. Merkel wanda ta yi wadannan kalaman bayan wani taron manema labarai da Firaministan Italiya Matteo Renzi da ya kai ziyara Berlin, ta ce dangantakarta da Firaministan Girka Alexis Tsipras ba ta yi rauni ba saboda rikicin bashin na Girka, tana kuma goyon bayan Girka a matsayin kasa mai 'yancin kai ta yanke ma kanta shawara.
"Na sha magana da Alexis Tsipras a kwanakin nan. A kullum ina nanata cewa hakkin kasa ne mai 'yancin kai ta yanke ma kanta shawara, ban taba shakkan wannan ba. Amma a hannu daya sauran kasashe 18 masu amfani da kudin Euro na da nasu matsayin. Amma za mu ci gaba da tattaunawa."
A wannan Laraba dai gwamnatin Girka ta mika sabuwar wasika ga hukumomin tarayyar Turai da ke birnin Brussels, sai dai ministan kudin Jamus Wolfgang Schäuble ya ce har yanzu ba ta canja zane ba.