Sifetocin Mdd sun isa koriya ta arewa
June 26, 2007Talla
Sifetocin hukumar IAEA sun isa yankin Fiyanyong din kasar koriya ta arewa. Wannan ziyarar dai ta kasance irin ta ta farko ne,a tsawon shekaru biyar da suka gabata.Tawagar ta Mdd na karkashin shugabancin Mr Olli Heinonen, wanda shine mataimakin daraktan hukumar kula da makamashin nukiliya ta duniya, wato IAEA.A cewar rahotanni tawagar ta IAEA zata shaida rufe tashar nukiliya ce taYongbyon, wacce mahukuntan na Koriya suka yi alkawarin rufewa a tattaunawar data gudana a tsakanin su da Amurka.A lokacin tattaunawar Amurka tayi alkawrin tallafawa kasar ta koriya ne wajen inganta harkokin makamashin ta.Ya zuwa yanzu dai tuni koriya ta kudu tayi alkawarin takllafawa makociyar kasar da tallafi na shinkafa, domin amfanin yan kasar.