Siriya ta ce za ta mayar da martani a kan Isra'ila
May 31, 2013Shugaba Bashar Al- Assad na Siriya ya ce ba shi da fargaba ko kaɗan a kan zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar a ƙasar a nan gaba, a shekara ta 2014. Wanda ya ce zai tsaya takara duk kuwa da halin yaƙi da ƙasar ta Siriya ta ke ciki.
Sannan kuma ya yi barazanar kai ramuwar gayya ga Isra'ila a kan duk wani farmakin da za ta kai a ƙasar ta Siriya bayan waɗanda ta kai har so uku a jere tun farkon wannan Wata. Shugaban ya bayyana haka ne a cikin wata hira da aka yi da shi a wani gidan Telbijan na Al-Manar na Hizbollah da ke a ƙasar Lebanon. Tun da fari shugaba Assad ya ce Rasha ta ba su kashin farko na makamai masu kakKaɓo jiragen sama na yaƙi. Abin da ya ce yana daga cikin kwangilar da Rasha ta samu daga garesu tun da daɗewa na sayar masu da makamai.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed Abubakar