Majami'u a Siriya sun jingine Kirsimeti don goyon bayan Gaza
December 24, 2023Majami'u a birnin Damascus na kasar Siriya sun takaita bukukuwan kirsimeti don nuna goyan baya ga al'ummar yankin Gaza da ke cikin tashin hankali sakamakon mamayar Isra'ila
Mor Dionysius Antoine Shahda da ke kasancewa shugaban cocin Aleppo, ya ce Falasdinu ce mahaifar annabi Isa, kuma yankin na cikin tashin hankali a halin yanzu, a don haka babu bukatar gudanar da wani babban biki kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Yankin Azizia da ke arewacin Siriya, waje ne da aka saba gudanar da kasaitaccen bikin kirsimeti tare da bude babbar kasuwar sayar da bishiyu da sauran kayayyakin kawa na bikin, to amma a bana babu kowa a wannan dandali.
Shugaban majami'ar ta Aleppo, ya kara da cewa sauran majami'un da ke sassan kasar ta Siriya sun takaita shagulgulan bukukuwan kirsimeti kamar yadda suka dauki mataki don nuna alhini kan al'ummar Gaza