1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya za ta kare kanta daga ko wanne hari

Ramatu Garba Baba
April 13, 2018

Kasar Siriya ta ce za ta dauki matakin kare kanta muddin kasashen yamma suka kai mata hari kamar yadda suka dauki alkawarin yi acewar jakadan kasar Bashar Jaafari a yayin taron kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya.

https://p.dw.com/p/2w1ur
Syrien Ost-Ghuta leere Raketenhülsen
Hoto: Getty Images/AFP/H. Mohamed

Jakadan ya ce wannan ba kalaman romon baka ba ne, alkawari ne Siriya ta dauka na yin abin da ya dace, ganin ba ta da zabi face ta mayar da martani kamar yadda dokar kasa da kasa ta tanadar na kare kai daga abokan gaba. Jaafari ya fadi hakan ne a yayin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ke nazarin warware takaddamar zargin Assad da anfani da makamai masu hadarin gaske.

Rahotannin sun nunar da cewa an tura tawaga ta musanman zuwa Siriyan, da ta kwashi shekaru fiye da shida ta na fama da yakin basasa don gudanar da cikakken bincike kan zargin. A yayin da ake ci gaba da samun sabanin ra'ayi kan wannan zargin kuwa, Amirka da kasashen Britaniya da Faransa na ci gaba da yin nazari kan matakin daukar fansa kan gwamnatin Bashar al-Assad bisa hannun a asarar rayukan da aka samu a yankin Douma a sanadiyar shakar iskar da ta gurabace da sinadarin Klorin. Rasha ta zargi Amirka da sa zaman lafiyan duniya a cikin hadari, inda ta nemi Amirkan da ta yi watsi da matakin kai wa Siriyan harin.