1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus sun dubi kasar Kenya da lafiyar Buhari

Mohammad Nasiru Awal MA
May 5, 2017

Shirye-shiryen zabe a Kenya da lafiyar Shugaba Buhari na Najeriya da kuma rashin tabbas kan siyasar Afirka ta Kudu sun dauki hankalin jaridun Jamus a wannan makon.

https://p.dw.com/p/2cSq6
Kenia Präsident Uhuru Kenyatta
Hoto: Reuters/T. Mukoya

Za mu fara da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda a labarinta mai taken an fara yakin neman zabe a Kenya ta ce:

Jam'iyyun adawa guda biyar sun kulla wani kawance da suka sanya wa suna "National Super Alliance" da ke da nufin kada gwamnatin shugaban kasa Uhuru Kenyatta da jam'iyyarsa ta Jubilee Party. Jaridar ta ce ba a taba samun irin wannan babban kawance a kasar ta Kenya ba, inda kabilanci ke taka rawa a fagen siyasa. Wanda zai tsaya wa kawancen 'yan adawa takara ba bako ba ne wato tsohon Firaminista Raila Odinga, mai shekaru 72 wanda sau uku yana shan kaye a kokarin nema shugaban Kenya. Zabe dai a kasar na yawan zuwa da rikici musamman bayan an baiyana sakamakon zabe. A shekarar 2007 akalla mutane 1100 aka kashe a rikicin da ya biyo bayan zabe. Ko da yake komai ya tafi salin alim a zaben da ya gabata a 2013 wanda Uhuru Kenyatta ya lashe da tazarar da ba ta taka kara ta karya ba, amma ba a sani ba ko a wannan karon za a yi irin wannan sa'a.

Jita-jita kan koshin lafiyar Shugaba Buhari

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung tsokaci ta yi kan rashin lafiyar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tana mai cewa lalle shugaban na fama da rashin lafiya.

Muhammadu Buhari Nigeria
An shafe makonni ba a ga Muhammadu Buhari a bainar jama'a baHoto: picture alliance/AP Photo/S.Alamba

Ta ce a karo na uku a jere Shugaba Buhari bai halarci taron mako-mako na majalisar kolin kasar ba da aka saba yi a kowace Laraba. Ta ce rashin halartar taron majalisar ministocin ya kara zafafa jita-jitar da ake game da koshin lafiyarsa. Buhari mai shekaru 74 a farkon shekara ya dauki hutun makonni da dama don duba lafiyarsa a birnin London na kasar Birtaniya, amma ya koma gida a cikin watan Maris. Har yanzu dai fadar shugaban kasar ba ta fito fili ta baiyana ainihin halin da shugaban ke ciki ba, amma a ranar Talata matarsa ta wallafa a shafinta na Twitter cewa rashin lafiyar mijintan bai kai yadda aka yayatawa ba.

Rikicin siyasa ya jawo koma baya na tattalin arziki

Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan makon ta leka kasar Afirka ta Kudu ne tana mai cewa rashin sanin tabbas a siyasar kasar ya janyo koma baya ga tattalin arzikinta da dama yake tangal-tangal.

Südafrika Präsident Jacob Zuma
Shugaba Jacob Zuma na shan matsin lamba daga 'yan adawaHoto: Getty Images/AFP/R. Jantilal

Jaridar ta ce ana ci gaba da aikin gine-gine babu kakkautawa, sai ka ce a lokacin bunkasar tattalin arziki, a Sandton da ke zama cibiyar hada-hadar kudi da ke birnin Johannesburg. Jaridar ta kara da cewa kamfanoni da bankuna da kantuna da kuma lauyoyi na rige-rigen kafa cibiyarsu a yankin. To sai dai wannan na zama wani hanzari ba gudu ba, domin yanzu haka yawancin masu zuba jari daga ketare sun fara ja da baya lamarin da ya shafi bunkasar tattalin arzikin kasar da yanzu yake bunkasa da kashi daya cikin 100, yayin da a sauran kasashen Afirka na Kudu da Sahara bunkasar ta kai kashi hudu cikin 100.