Siyasar Koriya ta Arewa
September 28, 2010Rohotanni dake fitowa daga Koriya ta Arewa na bayyana cewa, an zaɓi jagoran ƙasar Kim Jong a matsayin sabon shugaban jam'iyar da mulkin ƙasar. Labarin dai ya zo ne a bayan da yau aka buɗe taron wakilai na Koriya ta Arewa waɗanda suke taro mafi girma tun shekaru 30 da suka gabata. An dai yi raɗe-raɗin cewa, kafin kammala taro akwai alamun ayyana ɗan shugaba mai ci wato Kim Jong Un a matsayin wanda zai gaji mahaifinsa. A jiya dai gidan talavijin ɗin ƙasar ya ce an ƙarawa ɗan shugaban ƙasar muƙami izuwa Janar ɗin soja a rundunar sojojin ƙasar. Sake zaɓen da aka yi wa Kim Jong ya jagoranci jam'iyar kwaminisanci da ke mulkin ƙasar, wani nuni ne kan yadda har yanzu 'yan ƙasar ke ci gaba da yi masa biyayya, a dai adai lokacin da girma rashin lafiya haɗe da tsufe ke ƙara rage kuzarinsa.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Yahouza Sadissou Madobi