1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soja sun bi sahun Shugaba Jammeh a mika wuya

December 7, 2016

Shugaba Jammeh na Gambiya da ake wa kallon dan kama karya dai ya hana zanga-zangar adawa da ma shan alwashi na mulkin Gambiya shekaru ba adadi sai dai ya mika kai ba zata.

https://p.dw.com/p/2TvJ4
Yahya Jammeh 2006
Hoto: picture-alliance/AP/Rebecca Blackwell

Shugaban rundinar sojan kasar Gambiya ya bayyana cewa ya mika wuya ga zababben shugaban kasar Adama Barrow, kamar yadda mai magana da yawun Barrow ta bayyana a ranar Laraban nan, wani abu da ke nuna cewa wannan karamar kasar ta Yammacin Afirka ta tasamma mika mulki daga wata gwamnati zuwa wata cikin ruwan sanyi a sama da rabin karni. Janar Badjie dai ya kira Barrow inda ya taya shi murna da ma mara masa baya kamar yadda Amie Bojang, da ke magana da yawun Barrow, ta fada wa kamfanin dillancin labaran Reuters a birnin Banjul.

Hamshakin dan kasuwar, wanda ya taba zama mai gadi a shagon Argos a birnin London a shekarun baya, Barrow ya kai Shugaba Yahya Jammeh kasa a zaben da aka yi a kasar a ranar Alhamis da ta gabata. Jammeh ya bai wa 'yan Gambiya da ma duniya mamaki, bayan da ya amince da shan kayi, matakin da ya haifar da tarin tambayoyi a zukatan al'umma.