1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burkina Faso: Zargin soja da kisan fararen hula

April 24, 2023

Ana zargin sojojin Burkina Faso da kisan fararen hula sama da 60 a wani kauye da ake kira Karma wanda ke yankin Yatenga a kusa da iyakar kasar da Mali inda ake fama da haren-haren masu da'awa da makamai.

https://p.dw.com/p/4QTV1
Burkina Faso Ouagadougou Soldaten der Armee
Hoto: picture alliance / ASSOCIATED PRESS

Mai shigar da kara na kotun birnin OuahigouyaLamine Kaboré ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar da mairaican Lahadi 23.03.2023 bayan wani rohoton bincike da jam'ian tsaron jandarma suka mika wa kotu.

Mai shigar da kara ya ce ko baya ga mutane sama da 60 din da suka mutu da akwai karin wasu mutane da dama da ke kwance a gidajen asibi wadanda ake zargin sojojin da jikkatawa, ya kuma kara da yin kira ga wadanda suka shaida lamarin da bayar da gudummowa a kan binciken da aka fara domin hukunta duk wadanda ke da hannu a wannan aika-aika.

Wasu mazauna yankin da lamarin ya auku sun shaidawa kamfani dillancin labaran Faransa na AFP cewa a ranar Alhamis da ta gabata ne wasu mutane saye da kakin soja a cikin motoci da babura suka yi dirar mikiya a kauyen na Karma inda suka tabbacin kisan mutun kusan 80 matasa da kuma dattijai.

Wannan aika-aika dai na zuwa ne mako guda bayan mutuwar sojojin Burkina Faso shida tare da mayakan sa kai na VDP Dozo 34 da ake zargin masu dawa'a da makamai da kai masu hari a garin Aorema da ke da nisan kilomita 30 da kauyen na Karma inda masu hakar zinare ke tuturuwa a 'yan kwanakin nan.