1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Sojoji ke jagorantar kamfanonin gwamnati

Gazali Abdou Tasawa
November 10, 2023

A Jamhuriyar Nijar, wata mahawara ce ta taso a kasar a game da nade-naden manyan sojoji a jagorancin manyan kamfanoni da masana'antu da ma ma'aikatun gwamnati.

https://p.dw.com/p/4YfwR
 SOMAIR Kamfanin hako ma'adinin karfen uranium
SOMAIR Kamfanin hako ma'adinin karfen uraniumHoto: Joerg Boethling/IMAGO

 Tun dai bayan juyin mulkin da sojoji suka gudanar a kasar ta Nijar a ranar 26 gaw atan Yulin da ya gabata, shugaban hukumar mulkin soja kana shugaban kasa Janar Abdourahmane Tchiani ke ta nada sojoji a kan mukamai dabam-dabam na shugabancin ma'aikatu da kamfanoni da masana'antu na gwamnatin kasar wadanda ga al'ada fararan hula ke tafiyar da su. Wannan ce ta sanya wasu ‘yan kasar suka fara nuna damuwa kan yadda manyan sojojin ke neman tarewa a ofisoshi a cikin birane a daidai lokacin da aka fi bukatarsu a fagen daggar yaki da ta'addanci da kasar ke fama da shi. Malam Kane Kadaoure Habibou wani matashin dan siyasa dan takara a zaben shugaban kasar da ya gabata, da ke a sahun gaban kawo goyon baya ga sojojin da suka yi juyin mulki na daga cikin wadannan suka yi  wannan korafi.

Neman kawo gyara ko cin gajiya na mukamai ga sojojin Nijar

Niger Niamey | Abdourahamane Tiani
Hoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

 Shi ma dai Malam Sahnin Mahamadou wani na kusa da tsohon shugaban kasa cewa ya yi mika shugabancin kamfanonin gwamnati ga sojoji, alama ce na ba da gaske suke ba kan maganar tsaro.To sai dai wasu ‘yan kasar ta Nijar na ganin dacewar mika ragamar kamfanonin kasar ga sojojin wanda suka ce ba zai hana su kuma kula da harkar yaki ba.Yanzu haka dai wasu alkalumma wadanda ba na gwamnati ba na cewa akwai manyan sojoji sama da 80 da aka nada a irin wadannan mukamai na shugabancin kamfanoni da masana'antu da ma'aikatu na gwamnatin kasar ta Nijar daga juyin  mulki zoke yau.