Nijar: Sojoji sun musanta kisan dakarunsu
December 12, 2024Wasu kafafen yada labarai da kuma shafukan sada zumunta na zamani na Jamhuriyar ta Nijar ne dai, suka ruwaito mutuwar sojojin kasar 91 da fararen hula 47 a wani harin da 'yan ta'adda suka kai garin Chatoumane na yankin Tera da ke cikin jihar Tillabéri mai fama da barazanar tsaro. Kazalika labaran sun bayyana mutuwar wasu sojojin 43 a makon da ya gabata, suma yayin wani harin ta'addanci a yankin na Tera. Wannan na zuwa ne a daidai loakcin da wasu 'yan kasar ta Nijar ke nuna damuwa game da yadda 'yan ta'adda suka zafafa hare-hare a kan fararen hula, har ma da wasu garuruwan da ke babbar hanyar kasa a baya-bayan nan. Sai dai a wata sanarwa da rundunar sojojin kasar ta fitar da aka karanto a gidan Talabijin na kasa na RTN, ta karyata labarin.
Wannan sanarwa na zuwa ne a daidai loakcin da 'yan ta'adda ke zafafa kai hare-hare a baya bayan nan kan fararen hula, inda ko cikin wannan makon sun kona kauyen Libiri na kusa da karamar hukumar Samira cikin jihar ta Tillabéri. Sai dai Malam Siraji Issa na kungiyar Mojen ya ce, babban abun damuwa shi ne yadda matsalar ta'addancin ke yaduwa daga Tillabéri zuwa wasu jihohi da ma yadda 'yan ta'addan Mali da Nijar da Najeriya ke neman hadewa da junansu. Shi ko Malam Mouhamadou Gamatche shugaban kungiyar Direbobi ta Kasa nuna damuwa ya yi, a kan yadda matsalar tsaro ta soma yaduwa a babbar hanya ta kasa. Sai dai gwamnatin kasar ta Nijar ta tabbatar a hakumance da mutuwar sojojin kasar guda 10 a cikin hare-haren ta'addancin na baya-bayan nan a yankin na Tera wadanda tuni aka yi musu jana'iza, sabanin sama da 130 da wasu suka yada a shafukan sada zumunta.