Sojoji sun tabbatar da Juyin mulki a Jamhuriyar Nijar
July 27, 2023Sojojin da suka yi juyin mulkin sun kira kungiyarsu "Conseil National pour la Sauvegarde de la Patrie" CNSP wanda ke nufin kwamitin ceton kasa. Sun bayyana cewar sun kifar da zababbiyar gwamnatin saboda tabarbarewar harkokin tsaro da munmunan jagoranci a fannin tattalin arziki da na zamantakewa..
Amma Kanal Amadou Adramane da ke zama kakakin CNSP ya ce: "Muna jaddada goyon bayanmu ga dukkanin yarjejeniyoyi da dokoki na kasa da kasa da Nijar ta sanya hannu a kansu. Kazalika muna tabbatar wa al'ummar kasa da kasashen duniya cewa za mu kiyaye lafiyar mahukuntan da muka kifar kamar yadda dokokin kiyaye hakkin dan Adam suka tanada"
Kamar yadda sojoji suka saba yi ga al'ada bayan juyin mulkin, mambobin CNSP sun sanar da dakatar da hukumomin jamhuriyar Nijar da kuma yin bayanin yadda za a gudanar da ma'aikatun gwamnati. Kanal Amadou Adramane, kakakin CNSP ya ce: " An dora wa manyan daraktocin ma'aikatu gwamnati nauyin gudanar da al'amurra. Daga nasu bangare jami'an tsaro za su kula da tafiyar da al'amurra. Amma muna kira ga aminnan Nijar na ketare da kar su yi katsalandan cikin harkokin kasa."
Kazalika sojojin sun sanar da rufe iyakokin kasar tare da kafa dokar hana yawon dare a duk fadin kasa har zuwa lokacin da za su bayar da sabon umurni. Sojoji 10 ne ddaga rundunoni daban-daban suka bayyana a faifayen bidiyon sanarwar da juyin mulkin. Sai dai babu Janar Omar Tchiani wanda aka bayyana a matsayin jagoran juyin mulkin a cikinsu.
Wasu 'yan Nijar na adawa da juyin mulki
Duban jama'a sun shirya zanga-zangar kawo goyon bayansu ga Shugaba Mohamed Bazoum da kuma nuna adawa ga yunkurin juyin mulkin, Masu zanga-zangar sun yi yinkurin yin tattaki har zuwa fadar shugaban kasa, amma sojojin suka tarwatsa su ta hanyar harbi a sama. An gudanar da irin wannan zanga-zanga a wasu biranen kasar ta Nijar.