1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun yi ikirarin juyin mulki a Nijar

Mouhamadou Awal Balarabe
July 27, 2023

Wasu sojojin Nijar sun karanta sanarwar juyin mulki a kafar Talabijin din kasar ta RTN. Sun ce sun kafa dokar hana fita tare da rufe iyakokin kasar sannan suka rusa duk wasu hukumomin da ke karkashin mulkin farar hula.

https://p.dw.com/p/4UQsm
Lokacin da Shugaba Mohamed Bazoum ke tattaunawa da Yarima Frederik na DanmarkHoto: Mads Claus Rasmussen/Ritzau Scanpix/picture alliance

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta danganta yunkurin juyin mulki a Nijar da abin mamaki da ban takaici, inda a sanarwar da ta fitar ta yi kira ga wadanda suka aikata wannan aika-aika da su saki zababben shugaban jamhuriyar ba tare da wani sharadi ba. Ita ma a bangarenta, kungiyar Tarayyar Afirka ta AU, ta yi Allah-wadai da wadannan sojoji da ta ce sun ci amanar kasa da aka danka musu.

 Kungiyar Tarayyar Turai EU ma ta yi tir da abin da ta kira yunkuri kawo cikas ga dimukuradiyya da kuma yin barazana ga zaman lafiyar Nijar. Dama dai Jamhuriyar Nijar na daya daga cikin kawaye na kasashen yammacin duniya a yankin Sahel da ke fama da tashe- tashen hankula na masu da'awar jihadi.

Me sojojin da ke wannan yunkuri ke bukata?

Niger | Präsidentenpalast in Niamey
Tsohon Shugaba Issoufou ya yi kokarin shiga tsakani da askarawan fadaHoto: Ludovic Marin/AFP/Getty Images

Askarawan da ke tsaron fadar shugaban kasar sun ki sakin shugaba Mohamed Bazoum bayan da aka tattauna da tsohon shugaban kasa Mahamadou Issoufou. Amma rundunar sojin Nijar ta bada wa'adi kafin ta dauki matakn, a cewar wata majiya da ke da kusanci da fadar shugaban kasa. Ba a san abubuwan da sojojin ke bukata ba har i zuwa yammacin Laraba. Amma a wani sako da aka wallafa a shafin Twitter kafin a goge, fadar shugaban kasar Nijar ta danganta abin da ke faruwa da boren kin jinin jamhuriya.

Nijar ta yi kaurin suna a fannin juyin mulki

Juyin mulki ya zama ruwan dare a tarihin wannan kasa mai fadi da talauci da ke fuskantar kwararowar hamada. Tun bayan samun ‘yancin kai daga Turawan Faransa a shekarar 1960, an samu juyin mulki hudu a kasar: na farko a watan Afrilun 1974 inda aka hambarar da shugaba Diori Hamani, yayin da na karshe ya kasance a watan Fabrairun 2010 wanda ya yi sanadin hambarar da shugaba Mamadou Tandja.

Niger Niamey Ex-Präsident Tandja Mamadou
Tandja Mamadou ya zama shugaban karshe da aka yi wa juyin mulki a NijarHoto: DW/M. Kanta

Ko da a ranar 31 ga Maris, 2021, gwamnatin Nijar ta sanar da kame mutane da dama bayan wani yunkurin juyin mulki, kwanaki biyu kafin rantsar da shugaba Mohamed Bazoum. An kama wanda ake zargi da kitsa yunkurin juyin mulkin, Sani Gourouza, wani kaftain din sojojin sama, a makwabciyar kasar Benin tare da mika shi ga hukumomin Nijar.