Sojojin Mali sun kashe wani jigo a kungiyar IS
April 30, 2024Gidan talabijin mallakar gwamnatin Mali ya ruwaito cewa an halaka kasurgumin dan ta'addar mai suna Abou Houzeifa a yayin wasu samame da sojojin kasar suka kai a ranar Lahadin da ta gabata a yankin Meneka da ke Arewa maso gabashin kasar.
Karin bayani: 'Yan ta'adda sun kai hare-hare a wasu sansanonin sojan Mali
Shi dai Abou Houzeifa da ake kira Hugo ya kasance daga cikin wadanda suka tafka cin zarafin fararen hula a kasashen yankin Sahel, sannan kuma yana da hannu a harin kwantan baunar da ya yi ajalin sojojin Amurka hudu da na Nijar biyar a Tongo Tongo a shekarar 2017, har ma Washington ta saka tukwicin dala miliyan biyar ga duk wanda ya yi nasarar kamo mata shi.
Karin bayani: Rundunar tsaron hadin gwiwa a kasashen AES
Wata majiyar tsaro a Mali ta ce sojojin kasar sun samu tallafin abokan huldarsu na Rasha wajen gano mabuyar Abou Houzeifa da mayakansa da ke kai hare-hare da babura kafin daga bisani su fatattake su.