1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Nijar: Ba za mu wuce shekaru uku ba

August 20, 2023

Janar Chiani ya ce sojojin Nijar ba su zo da niyyar dawwama a mulki ba, amma ya yi gargadin idan har aka kai musu hari za su mayar da martani mai zafi.

https://p.dw.com/p/4VMSJ
Jagoran sojojin  Nijar Janar Abdourahamane Chiani
Jagoran sojojin Nijar Janar Abdourahamane ChianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

Sojojin Nijar sun ce ba za su wuce shekaru uku a kan karagar mulki ba. Wannan na kunshe a cikin jawabi na musamman da jagoran juyin mulki Janar Abdourahamane Chiani ya yi wa mutanen kasar a ranar Asabar da daddare. Janar Chiani ya ce za su yi kokari su mika mulki ga gwamnatin farar hula a cikin wa'adin da bai wuce shekaru ukun ba. Janar din ya ce ba su zo da niyyar dawwama a mulki ba, amma ya yi gargadin idan har aka kai musu hari za su mayar da martani mai zafi.

'' Ba za mu zura ido akai mana hari ba kamar yadda wasu ke tunani'' in ji Janar Chiani.

Gargadin nashi na zuwa ne a yayin da tawagar kungiyar bunkasa kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ta gana da shi a Asabar din nan, inda daga bisani jagoran tawagar Abdulsalami Abubakar ya shaida wa manema labarai cewa sun hango wata kofa da za a iya bude tattaunawa a tsakanin sojojin da ECOWAS wacce ta ce ta shirya aike wa da dakarun da za su dawo da dimkuradiyya a kasar.