1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Philippines sun kwace iko da Marawi

Abdul-raheem Hassan
October 23, 2017

Hukumomin kasar Philippines sun yi nasarar kakkabe 'yan bindiga da ake zaton mayakan IS tare da kwace iko da cibiyarsu da ke Kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/2mKZg
Philippinen Kampf gegen IS in Marawi
Hoto: picture-alliance/AA/J. Maitem

Nasarar kakkabe 'yan bindigan dai na zuwane bayan ba ta kashi tsakanin dakarun gwamnati da 'yan bindigan da suka kwashe sama da watanni biyar suna cunkushe a wani babban gini da suke tsare da wadan da suka yi garkuwa da su.

A yanzu dai ana kyautata zaton kawo karshen wannan fafatawa, zai tabbatar da murkushe yunkurin kungiyar IS da ke kokarin kafa sansanoni a rassa daban-daban a Kudancin birnin Marawi.

Ma'aikatar tsaron Philippines dai ta ce samun nasarar kwace ginin daga hannun 'yan tawayen, na zama wata babbar dama da zai ba wa sojojin kasar kwarin gwiwar maida birnin Marawi karkashin ikon gwamnati. Tun dai bayan jibge sojoji da nufin fatattakar 'yan bindiga a yankin na Marawi, an samu asarar rayukan mutane sama da dubu daya ciki harda 'yan bindigan da kuma wasu sojoji.