Sojojin Siriya sun kwace yanki a Aleppo
December 14, 2014Dakarun kasar Siriya sun sami nasarar kwace wani yanki na arewacin birnin Aleppo a yau Lahadi bayan wani gumurzu da bangaren mayakan sa ka. Kafafan yada labarai da ma kungiyar da ke sanya idanu kan rikicin kasar ne suka yi wannan bayani.
Birnni na biyu mafi girma a Siriya ya sami kansa cikin matsanancin fada tsakanin dakarun sojan gwamnati da na mayakan sari ka noke da mambobin kungiyar Al'kaida reshen na Siriya da ma 'yan aware da ke samun goyon bayan kasashen yamma.
Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a Siriya na ci gaba da kokarin ganin an samar da tsagaita wuta a birnin na Aleppo ta yadda za a samu damar kai wa ga dubban al'umma kayan agaji.
A cewar Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Siriya mai sansani a Birtaniya, dakarun na gwamnati sun kwaci yankin gabashin gonar Al-Malah dake wajen garin na Aleppo, suna kuma kokarin kwatar yammacin garin ta yadda zasu katse hanyar da 'yan tawayen ke iya kaiwa ga cikin birnin.